Tag Archives: Galadiman Illela

An ga Gawar Wannan Yarinyar Q Rataye A Cikin Gidansu

Screenshot_2018-04-06-13-15-45.png

Wannan lamarin dai ya faru ne da yammacin jiya, inda mahaifiyar marigayyar ta shaidawa wakilinmu cewar suna zaune suna hira bayan ta dora abincin dare sai ta ce bari ta je makota, fitar ta kenan bai fi minti 30 ba sai kawai ta jiyo ihu. Koda ta fito sai ta iske ta nufi gidan sai ta ga an taru, shigar ta ke da wuya sai ta ga ana sauko da gawar yarinyar maisuna Kadija. Continue reading An ga Gawar Wannan Yarinyar Q Rataye A Cikin Gidansu

GAISUWAR TA’AZIYAR MAMATA ISHIRIN DA TAKWAS (28) A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

Kamar yadda muka shaidama ma’abuta karatun Allonmu, a kwanakkin baya, , inda muka labarta maku bayanin mummunar hadarin Motar da ya faru ga ‘Yan Uwa Musulmi da ke kan hanyarsu ta zuwa Garin Chota, a cikin Jihar Dosso a Jamhuriyar Nijar. Continue reading GAISUWAR TA’AZIYAR MAMATA ISHIRIN DA TAKWAS (28) A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

INNALILLAHI WA’INNAILAIHIN RAJI’UN!!!

A Ranar Juma’a dai dai Sallar Assubah, Motochi guda biyu kirar Bus (SPORA) dauke da Mutane maza da mata wadanda suka tashi daga Karamar hukumar Mulkin Illela zuwa Garin Chota dake cikin Jihar Dosso, a Jamhuriyar Niger don kai Ziyara tare da gudanar da ababen Addininsu na Musulunchi kamar yadda aka saba lokutta daban daban, suka samu mummunan HATSARI a kusan Garin na Dosso, a sanadiyar kutsen da Direban wata Babbar Motar daukar Fasinja da ta taso daga Garin na Dosso ya yi. Continue reading INNALILLAHI WA’INNAILAIHIN RAJI’UN!!!