All posts by hayakionline

About hayakionline

Serving HUMANITY.

GAISUWAR TA’AZIYAR MAMATA ISHIRIN DA TAKWAS (28) A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

Kamar yadda muka shaidama ma’abuta karatun Allonmu, a kwanakkin baya, , inda muka labarta maku bayanin mummunar hadarin Motar da ya faru ga ‘Yan Uwa Musulmi da ke kan hanyarsu ta zuwa Garin Chota, a cikin Jihar Dosso a Jamhuriyar Nijar. Continue reading GAISUWAR TA’AZIYAR MAMATA ISHIRIN DA TAKWAS (28) A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

INNALILLAHI WA’INNAILAIHIN RAJI’UN!!!

A Ranar Juma’a dai dai Sallar Assubah, Motochi guda biyu kirar Bus (SPORA) dauke da Mutane maza da mata wadanda suka tashi daga Karamar hukumar Mulkin Illela zuwa Garin Chota dake cikin Jihar Dosso, a Jamhuriyar Niger don kai Ziyara tare da gudanar da ababen Addininsu na Musulunchi kamar yadda aka saba lokutta daban daban, suka samu mummunan HATSARI a kusan Garin na Dosso, a sanadiyar kutsen da Direban wata Babbar Motar daukar Fasinja da ta taso daga Garin na Dosso ya yi. Continue reading INNALILLAHI WA’INNAILAIHIN RAJI’UN!!!

Wani Darakta Ya Rataye Kansa Saboda Matarsa Ta Haifi ‘Yan Uku Kuma Gwamnatin Kogi Ta Hanashi Albashi Na Wata 11

Wani Darakta Edward Soje ya rataye kansa a bishiya a garin Lokoja da ke jihar Kogi. Mr Soje wanda ma’aikaci ne mai matakin albashi na 16 ya rataye kansa ne, kwanaki 10 da matarsa ta haifa masa ‘yan uku, kana kuma gwamnati ta hana shi albashi na tsawon watanni 11. Continue reading Wani Darakta Ya Rataye Kansa Saboda Matarsa Ta Haifi ‘Yan Uku Kuma Gwamnatin Kogi Ta Hanashi Albashi Na Wata 11

Buhari ya damu da goyon bayan da ISIS ke bawa Boko Haram

Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Alhamis ya ce ya kadu bayan da ya fahimci alakar dake tsakanin kungiyar Boko Haram da kuma ISIL.

A cewar,Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, Buhari ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Recep Tayyib Erdogan, shugaban kasar Turkiya bayan da suka gama ganawa a Ankara babban birnin kasar.

Shugaban na Najeriya ya ce ya yi farin ciki da ganin yadda gwamnatinsa ta samu nasarar shawo kan rikicin Boko Haram.

“Mun yi mamaki matuka da kuma damuwa kan ikirarin kungiyar Boko Haram na irin abin da suke samu daga ISIS,” yace.

” Mun san cewa zamu iya shawo kan matsalar, kuma mun nuna cewa zamu iya.

” Mun yi farin ciki da kasancewar Turkiya a wani matsayi da za ta iya taimaka mana dama ta dade tana taimakawa bangaren kiwon lafiyar mu da kuma ilimi.”

Shugabannin biyu sun kuma amince su kara karfafa dangantaka tsakanin hukumomin tsaron kasashen biyu domin yaki da ta’addanci.