Yan bindiga sun harbe mutane 20 mazauna wasu kauyuka dake Zamfara

Screenshot_2018-04-21-14-51-45.png

Wasu mutane da ake zaton barayi ne sun kashe akalla mutane 20 a wani hari da suka kai kan kauyukan Kadaro da Danmani dake karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

A makon da ya wuce mutane 26 aka kashe a wani hari makamancin haka akan kauyukan Kuru-Kuru da Jarkuka dake karamar hukumar Anka, a wani hari da ake zargin barayi dake dauke da makamai da kaiwa.

Harin kan kauyen Kabaro dake da tazarar kilomita 24 yamma da garin Dansadau na zuwa ne shekaru shida bayan da wasu barayin shanu da kuma yan bindiga suka kai hari garin inda suka kashe mutane 18.

Yankin na Dansadau dake fama da rikici na daya daga cikin yankunan da hare-haren barayin yafi kamari.Rikakken barawon shanu da ake kira Buharin Daji an kashe shi ne a wani daji daji dake kusa da garin na Dansadau ƴan makonnin da suka wuce.

Mazauna garin sun fadawa jaridar Daily Trust cewa tun da fari yan bindigar sun tare wasu mutane biyu dake kan babur akan hanyarsu ta zuwa kauyen daga Dansadau inda suka harbe su har lahira.

Haushin abin da yafaru yasa mutanen kauyen suka tattaru inda suka kama daya daga cikin yan bindigar kuma suka kashe shi a bayyanar jama’a.

Hakan ya harzuka yan bindigar inda suka dawo suka yi wa garin kawanya suka kuma fara harbin mazauna ciki bayan da suka toshe duk wace hanya ta barin garin.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s