Ni ne mutumin da zai gaji Buhari – Rochas Okorocha

Screenshot_2018-04-18-00-20-18.png

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce shine zai gaji shugaban kasa Muhammad Buhari.

Gwamnan ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a siyasar jihar, a gidan gwamnati dake Owerri.

Sun ziyarce shi ne domin nuna goyon bayansu ga, Uche Nwosu, shugaban ma’aikatan gwamnan, kuma mijin yarsa wanda shi ne matsayin mutunin Okorocha yake so ya kasance gwamnan jihar a nan gaba.

Okorocha ya ce bayyana aniyar sake tsayawa takara da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya yi wani abun cigaba ne kuma zai sake cin zabe kamar yadda ya yi a shekarar 2015.

“Buhari zai sake cin zabe. Bayan Buhari sai kuma yankin kudu maso gabas hakan na nufin lokacin Okorocha ne,” ya ce.

Mutane da dama daga ciki da wajen jihar na cigaba da nuna adawarsu ga yunkurin da gwamnan yake na tsayar da sirikinsa takara a matsayin mutumin da zai gaje shi.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s