An yi wa wani mutum bulala 80 saboda ya kira matar yayansa karuwa

Screenshot_2018-04-17-20-36-57.png

Wata kotun shari’ar Muslunci dake zamanta a Magajin Gari, jihar Kaduna a ranar Litinin ta yi umarni da a yiwa, Shuaibu Idris, bulala 80 bisa samunsa da laifin kiran matar yayansa, Suwaiba Abdulkadir, karuwa.

Suwaiba wacce ta shigar da kara kotun ta na zarginsa da bata mata suna inda ta ce Umar ya kirata karuwa bayan da suka samu sabani a tsakaninsu.

“Shuaibu kanin mijina ne mun samu sabani da shi har ta kai ga musayar kalamai inda ya kirani karuwa.

“Ina son wannnan kotu mai girma da ta yi min adalci domin abinda kanin mijina ya fada a kaina ya zubar mini da kima,”ta ce.

Mutumin da ake kara wanda bai musalta kiran matar ya yansa karuwa ba ya kara da cewa ya yi kalaman ne cikin fushi kuma baya dana-sanin fadin haka.

“Raina ya baci lokacin da ta ce min dan shaye-shaye kuma barawo shine dalilin da yasa nakira ta karuwa kuma bazan janye maganar da nayi ba,” ya ce.

Alkalin, Mallam Dahiru ya yanke hukuncin a yiwa Umar bulala 80 bayan da ya bashi damar ya janye kalmansa amma yaki.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s