Obasanjo bai isa ya hana Buhari cin zabe ba a 2019 – Shittu

Screenshot_2018-04-11-23-53-53.png

Adebayo shittu, ministan harkokin sadarwa ya ce tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo bai isa ya hana shugaban kasa Muhammad Buhari ba cin zabe a shekarar 2019.

Da yake magana da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN,ranar Talata a Abuja, ya bayyana aiyana sake neman wa’adin mulki karo na biyu da Buhari ya yi a matsayin wani cigaba da ake maraba da shi.

Shitu wanda shine jami’in tsare-tsare na wata kungiyar yaƙin neman zaben shugaban kasa Buhari a karo na biyu, ya yi kira ga magoya bayan shugaban kasar da su fara shirin tunkarar zaben.

“Wane ne Obasanjo?, Obasanjo ba Allah bane, IBB ba Allah bane, Obasanjo ya ta ba zama shugaban kasar nan ya so ya zarce zango na uku amma bai samu ba,” ya ce.

Shitu ya ce nasarar da shugaban kasar ya samu a shekaru uku ta shafe wacce jam’iyar PDP ta samu a tsawon shekaru 16 da ta shafe tana mulki.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s