Za mu kai karar Buhari idan ya ki sake tsayawa takara – Ganduje

Screenshot_2018-04-07-01-13-08.png

Gwamnan jihar Kano, Abudullahi Umar Ganduje ya ce za a kai karar shugaban kasa Muhammad Buhari gaban kotu idan har yaki tsayawa takara  a shekarar 2019.

Da yake magana da yan jaridu ranar Juma’a,a Abuja, Ganduje ya ce dukkanin gwamnoni da aka zaba a karkashin jam’iyar APC suna so Buhari ya cigaba da mulki.

Gwmnan ya yi karin haske cewa babu wani abu na rashin dai-dai idan shugaban kasar ya nemi zango na biyu da tsarin mulki ya bashi.

“Gwamnonin APC suna son shugaban kasa ya cigaba.Ina farin ciki cewa ba shugaban kasa bane ya ce yana son ya cigaba, mutane ne suke sonsa ya cigaba  amma har yanzu shugaban kasa bai yanke shawara ba,”ya ce.

“Lokacin da ya zo Kano, na fada masa cewa duk lokacin da ya yanke hukuncin ba zai tsaya takara ba za mu kai shi kara gaban kotu.Gwamnatin Kano za ta kai shi kara gaban kotu duk lokacin da yanke shawarar ba zai tsaya takara ba saboda haka muna jiransa.”

Sourced by : Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s