Asirin Wani Mai Ɓata Ƙananan Yara Ya Toni A Birnin Kebbi

Screenshot_2018-04-06-00-33-26

A yau alhamis 5/4/18 ‘yan kungiyar banga suka kama wani mutum mai suna Abdul-Aziz Muhammad Jega mai kimanin shekaru 35 da haihuwa, wanda ake zargi da boye wasu kananan yara mata su 4 masu kimanin shekara 8 zuwa 12.

‘Yan bangar sun mika shi ga hukumar Hisbah ta jihar Kebbi domin gurfanar dashi gaban kotu.

Da yake amsa tambayoyi daga jami’an Hisbah Abdul-Aziz ya amsa laifin da ake zarginsa na boye kananan yara mata da kuma lalata da su, inda ya bayyana cewar ya jima yana wannan mummunan aiki sai yau ne dubun sa ta cika.

Alhaji Abubakar Muhammad Augie Daraktan Sharia a ofishin Hisbah ya gabatar da mai laifin gaban ‘yan jarida da kuma kungiyoyin mata, tare da yin Allah wadai da wannan lamarin.

Ya kuma bayyana cewar za su gufanar da shi gaban kotu don fuskantar shari’a.

Alhaji Suleiman Muhammad shugaban hukumar Hisbah ya yi kira ga uwaye mata da su guji azawa yaransu tallace tallace domin shine tushen lalacewar ‘ya’ya mata.

Mukaddashin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara ta jihar Kebbi wato (WRAPA) Malam Nasir idris ya bayyana cewa kungiyarsu za ta bi shari’ar a kowanne mataki, don ganin an hukuntar da shi yadda doka ta tanada.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s