An gaza samun dai-daito a ganawar da Buhari ya yi da gwamnonin jam’iyar APC

Screenshot_2018-04-05-00-19-34

An tashi baran-baran  a ganawar da aka yi tsakanin shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma gwamnonin jam’iyar APC a jiya Talata.

Babu daya daga cikin gwamnonin da ya gana da  yan jaridar dake dauko rahoto daga fadar shugaban kasa lokacin da suke ficewa daga dakin da aka gudanar da  taron dake fadar shugaban kasa.

Rochas Okorocha, gwamnan jihar Imo, Simon Lalong, na jihar Plateau da kuma Nasir El-Rufai na jihar, Kaduna sun fadawa manema labarai cewa an cimma yarjejeniyar kada kowa daga cikin gwamnonin ya yi wa kafafen yada labarai jawabi.
A lokacin da yake fita daga wurin taron an ji yo daya daga cikin gwamnonin na cewa “Wasu mutane suna tunanin suna da tsawo, to baza su iya juyamu ba, ba zai taba yi yuwa ba.”

An dai gudanar da taron ne domin tattaunawa kan batun tsawaita wa’adin mulkin shugabannin jam’iyar.

 

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s