Za’a Binciki PDP Bisa Zargin Yi Wa Buhari Kutse Da Satar Bayanan Sa

Screenshot_2018-04-01-11-16-42

Gwamnatin tarayya za ta binciki yadda jam’iyyar PDP ta yi hayar wani kamfanin Isra’ila wanda ya yi mata kutse wajen tattaro duk wasu bayanan sirri da suka shafi Shugaba Muhammad Buhari a kakar zaben 2015.

PDP dai ta biya kamfanin milyoyin Nairori don ya yi mata kutse a kundin bayanan jami’ar Cambridge wanda a can baya shi ke shirya jarrabawar kammala sakandare na daliban Nijeriya wanda kuma ke da Cikakkun bayanai kan kowane dalibi wanda ya hada har da abin da ya shafi lafiyarsa.

Irin wannan kutse ne ga bangaren adawa ya janyo Shugaba Nixon na Amurka ya yi murabus don kafin a tsige shi kuma a halin yanzu ana Bincken gwamnatin Rasha kan rawar da ta taka wajen yin kutse a zaben Amurka wanda hakan ya ba Shugaba Donald Trump samun damar lashe zabe.

A bangare daya kuma, jam’iyyar PDP ta karyata Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu bisa ikirarin da ya yi cewa ya taka rawa wajen murde zabe a lokacin da suke mulki inda jam’iyyar ta nuna cewa ba ta taba umartar wani dan jam’iyyar kan ya murde zabe ba.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s