Duk wanda ya ke korafin yunwa yaje ya nemi aiki -Garba Shehu

Screenshot_2018-04-02-19-35-36

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya yi kira ga mutanen da suke korafin da akwai yunwa a kasa da su je su nemi aiki.

A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Ben, Shehu ya ce gwamnati mai ci ta zuba kudi masu yawa wajen samar da abubuwan more rayuwa da kuma cigaban jama’a.

“Duk wanda yake korafin yunwa yaje ya yi aiki.kuma kasan cewa wannan gwamnatin ce kadai ta fara bijiro da tsarukan bunkasa rayuwar mutane muna biyan kudi ga mutane da suka fi talauci, mafi karancin abinda suke karba shine   ₦ 5000.”

Shehu ya ce tun lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya hau kan mulki yana ware abin da bai gaza kaso 30 ba cikin  dari na kasafin kudi wajen samar da abubuwan more rayuwa.

Sourced by: Galadiman Illela

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s