Mutane 4 sun mutu 13 kuma suka jikkata a harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri

Screenshot_2017-08-06-18-16-07

A kalla mutane hudu ne  suka mutu wasu 13 kuma suka jikkata ciki har da wani Farfesa ya yin da wasu yan kunar bakin wake suka kai hari a birnin Maiduguri. a daren jiya, a cewar mazauna yankin da kuma Civilian JTF.

Ƴan kunar bakin wake da ake zaton yayan kungiyar Boko Haram  ne sun isa yankin Muna Zauyar a karamar hukumar Mafa dake babban birnin jihar da karfe 8:45 na dare inda suka kashe wata mata, akuyoyi hudu da kuma kare daya wasu mutane da dama kuma suka jikkata.

“Mace guda ta rasa ranta, wasu mutane 13 kuma sun jikkata ciki har da Farfesa Khursa Imma na tsangayar karatun shari’a a Jami’ar Maiduguri wanda ya samu rauni tare da yayansa biyu inda suke karbar magani a asibitin koyarwa na jami’ar  Maiduguri,”  acewar wata majiya dake Civilian JTF ta shedawa jaridar Daily Trust.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Borno, DSP Edet Okon ya tabbatar da faruwar harin cikin wani sako da ya aikewa manema labarai.

Sourced by: Galadima

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s