Dino Melaye ya kai ziyarar ta’aziya a Abuja duk da nemansa da rundunar yan sanda ke yi 

Screenshot_2018-03-31-18-15-54

Dino Melaye sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, a ranar Juma’a ya kai ziyarar ta’aziya gidan Umar Jibrin dan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar mazabar Kogi/Lokoja da Allah ya yi wa rasuwa.

Jibril ya mutu bayan gajeriyar rashin lafiya a gidansa dake Abuja.

Yan majalisar wakilai da kuma takwarorinsu na majalisar dattawa na ta tururuwa ya zuwa gidan domin yi wa iyalansa ta’aziya.

Rundunar yan sanda ta bayyana Melaye a matsayin mutumin da take nema ruwa a jallo.

Hakan ya biyo bayan tserewar da wasu mutane suka yi daga hannun yan sanda.

Mutanen da suka tsere sun zargi Melaye da saya musu makamai.

Zargin da Melaye ya musalta inda ya yi kira ga  rundunar lallai ta nemo mutanen da suka tsere.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s