INNALILLAHI WA’INNAILAIHIN RAJI’UN!!!

A Ranar Juma’a dai dai Sallar Assubah, Motochi guda biyu kirar Bus (SPORA) dauke da Mutane maza da mata wadanda suka tashi daga Karamar hukumar Mulkin Illela zuwa Garin Chota dake cikin Jihar Dosso, a Jamhuriyar Niger don kai Ziyara tare da gudanar da ababen Addininsu na Musulunchi kamar yadda aka saba lokutta daban daban, suka samu mummunan HATSARI a kusan Garin na Dosso, a sanadiyar kutsen da Direban wata Babbar Motar daukar Fasinja da ta taso daga Garin na Dosso ya yi.

Wannan hadarin yayi sanadiyar Mutuwar Mutane Ishirin da bakwai (27) tare da jikkita wasu da dama. Dukkan wadanda abin ya shafa, sun fitone daga garin Amarawa da Gidan Tudu duk a cikin Karamar Hukumar Mulkin Illela, dake cikin Jihar Sokoto.

Jim kadan da samun wannan labari, Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela (Alh. Abdullahi Haruna Illela), Alh. Sahabi Isah Illela (Wakilin Maigirma Sarkin Rafin Illela), Shugaban Jam’iyar APC na Karamar hukumar mulkin Illela (Alh. Muhammadu Musa Sarkin Alaru) Galadiman Illela (Alh. Aminu A. Musa Illela) da Alh. Mustapha Mai Atamfa suka garzaya zuwa Garin na Dosso don bada agaji ga wadanda suka jikkita tare da halartar Sallar Jana’izar wadanda suka rigamu gidan GASKIYA.

An gudanar da Sallar zana’izar Mamatan bayan Sallar Juma’a a garin Chota, kuma an aikata dukkan ababen da Addinin Musulunchi ya gindaya akan mamatan a garin na Chota tare da halartar dubban Mutane da Jami’an Gwamnatin ta Jamhuriyar Niger.

Hakazalika dukkan wadanda suka samu raunukka sun samu kulawa ta musamman a babbar Assibitin Gwamnati dake a Garin na Dosso.

Haka kuma tawagar Maigirma Shugaban karamar hukumar mulkin Illela ta samu tarbo da kulawar Ministan Sufuri na Jamhuriyar Niger a matsayin wakilin Shugaban Kasar ta Jamhuriyar Niger (Muhammadu Yusuf) tare da Maigirma Gwamnan Dosso (Ousmane Moussa) don nuna alhinin iftila’in da ya faru ga ‘Yan Uwa Musulmi.

A lokacin da yake jawabinsa, Maigirma Gwamnan Dosso (Elhj. Ousmane Moussa) ya gudanar da Addu’ a ta musamman ga mamatan tare da jajantawa Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela, da ‘Yan Uwan Mamatan da al’ummar Jihar Sokoto baki daya akan wannan rashi. Haka kuma ya shaidama tawagar ta Maigirma Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela cewa Gwamnatinsa zata ci gaba da bada kulawa ga majiyatan dake kwance a Assibiti.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s