GAISUWAR TA’AZIYAR MAMATA ISHIRIN DA TAKWAS (28) A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

Kamar yadda muka shaidama ma’abuta karatun Allonmu, a kwanakkin baya, , inda muka labarta maku bayanin mummunar hadarin Motar da ya faru ga ‘Yan Uwa Musulmi da ke kan hanyarsu ta zuwa Garin Chota, a cikin Jihar Dosso a Jamhuriyar Nijar.

Wannan mummunan Hadari da yayi sanadiyar mutuwar Mutanen Garin Amarawa da Gidan Tudu, duk’ Yan Karamar hukumar mulkin Illela, Jihar Sokoto.

Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela (Alh. Abdullahi Haruna Illela), Sakataren Karamar hukumar mulkin Illela (Alh. Murtala Madawaki Yabo), Daraktocin sashen Lafiya, Jindadin Jama’a tare da Maigirma Wakilin sarkin Rafin Illela (Alh. Sahabi Isah Illela), Sa’n Illela (Alh. Yusuf Haruna Illela), Turakin Illela (Alh. Hassan Dan Larabawa), Sarkin Igbo (Mr. Okoh Jumbo), Galadiman Illela (Alh. Aminu A. Musa Illela), Maigima Shugaban Jam’ iyar APC na Karamar hukumar mulkin Illela (Alh. Muhammadu Musa Sarkin Alaru) da Babban limamin Masallacin Juma’a na Illela (Mal. Salihu), sun je garuruwan Rangandawa don gaisuwar Ta’aziyar mutuwar Limamin Garin Mallam Bello Rangandawa, da kuma Garin Gidan Tudu da Amarawa, musamman Gidan Khalifa Hayatu Amarawa wanda yayi hasarar Iyalansa goma (10) cikin wannan mummunan HADARIN Mota.

A lokacin wannan ziyara, Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela ya gabatar da buhuhuwan Shinkafa don ciyarda Iyalan Mamatan.

Allah ya jikansu da rahmarsa

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s