Babban Sifeta yan sanda ya  sayawa Aisha Buhari motoci biyu – Misau

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojan ruwa, Sanata Isa Hamma Misau, ya zargi babban sifetan yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, da sayawa matar shugaban kasa Aisha Buhari, motoci biyu kirar Prado.

Misau yayi wannan zargin ne lokacin da ya bayyana gaban kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa da zai binciki rikicin da sanatan yake da babban sifetan janar din yan sanda na kasa.

Ya ce Aisha Buhari ta nemi da a bata motoci biyu kirar Hiace da Siena ta hannun odilan dinta amma babban sifetan yan sandan sai ya bata motoci biyu kirar Prado.

Ya kuma yin zargin cewa babban sifetan ya sauya lokacin barin sa aiki ta hanyar jirkita jerin sunayen jerin sunayen ma’aikata.

Shugaban kwamitin na wucin gadi kuma mataimakin bulaliyar majalisar, Francis Alimikhena ya ce babban sifetan yan sandan za bayyana gaban majalisar mako mai zuwa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s