Jihohi 4 ne za su ‘ iya biyan albashi ba tare da sun ciwo bashi ba

Jihohi hudu ne kacal a Najeriya za su iya biyan albashi ba tare da sun ciwo bashi ba, hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da wata kungiya mai suna  BudgIT da ke sa ido kan yadda gwamnatoci ke kashe kudade.

An kaddamar da rahoton ranar Alhamis inda aka sake shi ga jama’a rana Juma’a.

Jihohin Kano, Katsina, Lagos da kuma jihar Rivers na daga cikin jihohin dake kan gaba cikin jerin alkaluman da aka saki.

Wadannan jihohi su ne kawai suke iya biyan albashi da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum ba tare da sun ciwo bashi ba ko kuma sun nemi tallafin kudade ba.

Rahoton yayi nuni kan yadda bashi ya yiwa wasu jihohi katutu musamman jihohin, Lagos, Cross Rivers da kuma jihar Osun.

Rahoton ya bayyana jihar Kwara a matsayin jihar da kudin shigar da take tarawa ke karuwa sosai.

Har ila yau rahoton ya bayyana jihohi Delta, Kebbi, Gombe da kuma Ebonyi a matsayin jihohin da bashin da ake binsu ya ragu sosai.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s