Wani dalibi zai karbi hukuncin bulala 6 

Wata kotu dake Karmo, Abuja, ranar Tuesday, tayi umarni a yiwa wani dalibi, mai suna Mudassir Ibrahim dan shekara 18, bulala  6 .

Ibrahim dake zaune a unguwar Hausawa Karmo ya amince da dukkanin laifu uku da ake tuhumarsa da shi inda ya roki alkali da ya sassauta masa.

Alkalin kotun, Alhaji Abubakar Sadiq,ya bada umarnin bayan mai laifin ya amince da laifinsa.

Sadiq ya umarci Ibrahim mai laifin da ya biya kudi ga mutumin da ya shigar da karar kana ya garagde shi da ya guji aikata haka anan gaba.

Ya ce kotun baza ta sassauta masa ba idan ya sake aikta laifi makamancin haka anan gaba.

Mai gabatar da kara, Florence Avhioboh ta fadawa kotun cewa wani mutum Mustafa Ibrahim dake Karmo shine ya  kai rahoton faruwar lamarin gaban ofishin yan sanda.

Tace mai laifin ya daki mai kara gaban a kafada da zimmar neman suyi fada lokacin da mai karar yake tsaye a kofar shagon mai laifin amma sai jama’a suka hana shi.

Amma daga baya sai gayyato abokinsa wanda yanzu haka ya ranta a nakare inda suka yi masa duka har takai da ya kashe ₦10500 wajen maganin raunin da suka yi masa.

Avhioboh tace laifin ya saba da sashi na 79,265 da kuma na 247 na kudin shari’ar penal code

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s