Farashin Babban Buhun Shinkafa Zai Dawo ₦6000

Aminu Goronyo shugaban Kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya, AFAN yace nan da yan watanni kadan masu zuwa za a siyar da buhun shinkafa kan kudi ₦6000 ko wanne buhu mai nauyin kilogiram 50.

Goronyo yayi wannan magana ne a wurin taro da ministan aikin gona Audu ogbeh yayi da manoman a da kuma masu sarrafa ta a hedkwatar ma’aikatar dake Abuja.

Ya alakanta samun faduwar farashin da ake sa ran samu da albarkar kaka da aka samu a bana.

Yace masu harkar shinkafar sun amince su rage kudin kowanne buhu mai nauyin kilogiram 50 daga ₦15000  zuwa ₦13000 kan kowanne buhu.

“Wannan yanzu aka fara. Amma cikakken farashin zai yi kasa da haka sosai saboda albarkar noma da aka samu a bana mun zauna da masu zazzabe shinkafar mun kuma amince zamu yi aiki tare domin kare hakkin yan Najeriya,”yace.

” A baya mutane suna siyan buhun shinkafar kan kuɗi ₦18000 amma yanzu ana siyanta ₦15000 zuwa ₦13000, farashin yana yin kasa sosai.

“Nan da watanni kadan masu zuwa da izinin Allah buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 sai ya dawo ₦6000. Abune mai yi yuwa tabbas zai zama gaske,” yace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s