n
A kasar China inda ake fama da matsananciyar matsalar karancin mata, wani matashi ya yanke al’aurarsa don kubutar da kansa daga ukubar gwauranci.
Mutumin mai kimanin shekaru 25 da haihuwa wanda mazaunin garin Jiaxing ne da ke kusa da babban birnin kasar Beijing.
Matashin ya sanarwa manema labarai cewa ya yi hakan ne domin ya kubutar da kansa daga kuncin kadaici, likitoci sun yi kokarin kawo wa matashin dauki amma kuma hakar su bata cimma ruwa ba.
Dan Chinan ya yanke wa kansa wannan danyen hukuncin ne domin ya ce yana da tabbacin zai kasance gwauro har karshen rayuwarsa.
Kasar Sin na fama da matsananciyar matsalar karancin mata, wacce ta samo asali daga tsarin haihuwa na da daya tilo, da kuma hallata wa jama’a zub da ciki musamman ma idan abinda za a haifa mace ce.
Yanzun haka dai akwai maza kusan miliyan 40 a kasar ta China da ke fama da rashin aure.