TARON MASU RUWA DA TSAKI NA KUNGIYAR MUTAWALLE SAK

Wanda aka gabatar a yau ranar Lahadi 24th Satumba 2017 a Babban Ofishinta dake kan Titin Kwannawa a babban Birnin Jihar Sokoto.

Wannan zaman shine na farko bayan sabunta shugabancin ita.

A sa’ilin da take vabatar da taronta, wannan kungiya ta samu damar bayyana cewa banban dalilin kafa wannan kungiya shine bayyanar da manufofin da cigan da wannan GWAMNATIN MAI GIRMA MATAWALLEN SOKOTO ta samar ga Al’ummar Jihar Sokoto.

Shugaban wannan Kungiya Alh. Aliyu Abubakar Philisco (Matawallen Dange) a lokacin da yake gabatar da
Jawabinsa, ya tabbatar da gudanar da ayukka tukuru don ganin wannan Kungiya ta aiyanar da dukkan kudurorinta.

Hakazalika, Sakataren Kungiyar ya nanata samuwar wannan Kungiya a cikin dukkan Kananan Hukumomin dake cikin jihar nan.

Wannan kasaitaccen taro, ya samu halartar masu fada aji daga cikin wannan Gwamnati da ma Jam’iyya mai mulki daga cikinsu akwai Shugaban Kungiyar Alh. Aliyu Abubakar Philisco, Mai Girma Kwamishina Lafiya na Jihar Sokoto Alhaji Shehu Kakale, Hon. Alhaji Dayyabu Adamu Kalmalo (Member State House Sokoto), Sakataren Karamar hukumar mulkin Sokoto ta Kudu Alhaji Ibrahim Ardo Shuni, Alh.  Aminu A. Musa (Galadiman Illela),  Alh. Umar Walin Gwadabawa da sauransu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s