Rahoton Juma’a: Mutumin Banza Ne Kadai Ke Dukan Matarsa – Kabiru Gombe

Mutumin da tausayi da rashin bin koyarwar Manzon Allah Muhammad(SAWW) kadai ne zai iya zagewa ya duki matarsa. 

Wannan tunatarwa ta fito daga bakin Sheikh Kabiru Gombe ne a yayin da ya ke amsa tambayoyin Zuma Times Hausa game da hukunci dukan mace a Musulunci inda ya kara da cewa, “iya rayuwar Manzon Allah (SAWW) bai taba daga hannu ya duki mace ba saboda haka duk lokacin da wani zai duki mace ya kudurta a ransa ba da Manzon Allah ya ke koyi ba.

“Sannan kuma akwai lokacin da mutane biyu suka zo neman aure, Annabi Muhammad(SAWW) Ya yi bishara da cewa kar matar ta auri dayan saboda da shi mai dukan mace ne.”

Malam ya ce, Manzon Allah (SAWW) yana cewa “ba za ka ji kunya ba bayan ka duke ta sannan ka nemi ka yi kwanciyar aure da ita bayan kauna da soyayya ne ke kawo shi? ”

Malamin ya kara da cewa yawancin masu jingina dukar mace da abinda Al-Kur’ani ya fada,  ba su cika sharudan da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba don kuwa da sun bi sharudan da kila ba za a kasance an kai ga duka ma ba.

Malam Kabiru Gombe ya kawo sharudan da Al-Kur’ani ya bayar kafin dukan da kuma yadda a ke dukan kamar haka:

“Matar da ba ta bin umurnin miji, mai taurin kai,  ta hana miji zama lafiya ta hana gida zaman lafiya sai Allah Ya ce, a yi mata wa’azi shine mataki na farko ba duka ba.

“In ta ki jin wa’azi sai Allah Ya ce mataki na biyu,  Allah Ya ce ka kaurace mata a wajen kwanciya. Hikimar haka ita ce in akwai tsoron Allah da imani kuma tana sonka kuma ta ga irin kaunar da ka ke mata kafin ta yi laifi,  dama ka saba kana tarairayarta kamar sarauniya, kana nuna mata kauna sai ka janye, ta ga ko kallonta ba ka son yi, wajen kwanciya ka juya mata baya dalilin abinda ta yi,  to dole ta fahimci cewa ba ta kyauta ba, in mai imani ce ba kangararriya ba sai ta ga ya kamata ta gyara.

“Mataki na uku shine in har aka kawo wannan mataki ba ta gyara ba,  to a nan ne Allah Ya ce kun iya dukansu amma malamai sun yi bayani game da yadda dukan ya ke.

“Yadda dukan ya ke,  ba wai kawai za ka dunkula hannu ko samu bulala ka yi ta kai mata duka ba don ba a taba samun mutumin kirki a tarihin Musulunci da  ya yi hakan ba. Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara  tabbata a gare Shi,  ya ce, ‘babu mai girmama mata sai mutumin girki,  babu mai walakanta su sai mutumin banza.

“Wani har sai ya yi bisimillah ya kai wa matarsa mari ko ya yi mata bulala,  to irin wannan shine mutumin banza a harshen Manzon Allah(SAWW).”

Malam ya kara da cewa, in  an cika sharuda da Allah Ya bayar kafin a tabe ta,  to ya kasance,  dukan ba zai karya mata kashi ba, dukan kuma ba zai kumbura mata fata ba, ba zai fasa jikinta na,  wannan shine dukan tarbiya.

@Galadiman Illela.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s