EFCC Na Shirye Shiryen Dawo Da Madueke Gida Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-kasa, EFCC ta tabbatar da shirin taso keyar tsohuwar Ministan mai, Diezani Alison Madueke daga Ingila zuwa Nijeriya.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan Nijeriya suka bukaci hukumomi da su taso keyar tsohuwar Ministar saboda zargin ta da cin hanci da rashawa.

Tuni dai, kotu da mallaka wa gwamnatin Najeriya wasu kadarori na biliyoyin Naira da aka kwato daga hannun Madueke bayan ta tara su ta haramtacciyar hanya.

Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ce, suna kan gudanar da bincike game da taso keyarta kuma wadanda ake zargi da cin hanci ba za su tsira daga fuskantar hukunci ba.

Magu ya kara da cewa, a yanzu, sun kai matsayin da babu wanda zai dakatar da su a yakin da su ke yi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, kuma suna wannan aikin ne don amfanin al’ummar da za ta zo nan gaba.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s