Dangantaka Tayi Tsami Tsakanin Ali Nuhu Da Rahma Sadau 

Dangantaka tsakanin jarumi Ali Nuhu da Rahma Sadau tayi tsami saboda kin sakata a wani sabon fim da yake kan yi yanzu mai suna “Abota”. Rahma Sadau wacce kungiyar masu shirya fina-finai ta MOPPAN ta dakatar daga fitowa a duk wani fim na Hausa. Sai dai fitacciyar jarumar ta fito a cikin wasu fitattun fina-finan Hausa da jarumi Ali Nuhu, ya shirya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jarumar taji haushi ne saboda gazawar fitaccen dan wasan kwaikwayon na bata wani matsayi cikin fim din da yanzu haka yake aikinsa.

Sabanin da   yafaru ya jawo zazzafar muhara a tsakanin magoya bayan yan wasan kwaikwayon biyu, a kafafen sadarwar zamani.

Wasu daga cikin magoya bayan sun dora laifin sabanin da aka samu akan Sadau inda suka zargeta ga nuna dagawa da kuma girman kai ga Ali Nuhu, wanda shine ubangidanta a harkar fim.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s