Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Gamsuwarta Da Aikkn Hajjin Bana

Gwamnatin tarayya ta bayyana gamsuwa bisa cigaban da aka samu wajen tafiyar da ayyukan Hajjin bana, tare da kira ga masu ruwa da tsaki a hidimar aikin Hajjin su kara nuna himma da kwazo, domin dorewar wannan nasara da aka samu. 

Karamar ministar kula da harkokin kasashen waje, Hajiya Hadiza Abba Ibrahim ita ta bayyana haka a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar bayan kammala aikin Hajjin, domin tsara yadda za a mayar da alhazan Nijeriya gida.

Hajiya Hadiza, wacce jakadan Nijeriya a kasar Saudi Arabia Ambasada Halliru Sodangi Shu’aib ya wakilta, ta bayyana cewa, lallai a bana an samu canje canje masu yawa fiye da na shekarun baya.

Ta ce, cigaban da aka samu ya zama kalubale ga shugabannin hukumar kula da ayyukan Hajji don su ga sun dora kan nasarorin da aka samu ba tare da gazawa ba.

Da yake jawabi a taron shugaban hukumar NAHCON Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar, wanda ya godewa Allah bisa wadannan nasarorin da aka samu, ya yabawa hukumomin kasar Sa’udiyya, hukumomin kula da walwalar alhazai na jihohi, masu ruwa da tsaki gami da alhazan kansu da gudunmawar da kowa ya bayar har aka samu nasarorin da aka cimma, kawo yanzu, inda ya ce ba za a ce an kammala aiki ba har sai kowanne Alhaji ya koma wajen iyalan sa lafiya.

Ya kuma yabawa ofishin jakadancin Nijeriya, hukumar NAHCON da sauran ma’aikata da irin hadin kai da goyon bayan da suka bayar cikin saukin kai da sadaukarwa saboda Allah, don tallafawa alhazan da suka samu matsaloli yayin aikin Hajjin.

A cikin jawaban da suka gabatar kwamishinonin kula da ayyuka da na kudi, Alhaji Abdullahi Saleh Modibbo da Alhaji Adebayo Yusuf duk sun yi bayanin ayyukan da ofisoshin su suka gudanar da suka hada da samar da masauki mai kyau, abinci da zirga-zirga, wanda a baya ba a taba samun su da kyau haka ba. Sannan har wa yau ga shi kuma an fitar da jadawalin fara jigilar komawa gida da wuri, duk domin a samu damar kammala komai cikin tsari ba tare da wata tangarda ba.

Mai magana da yawun bakin hukumomin kula da walwalar mahajjata na jihohin kasar nan Alhaji Abu Rimi shi ma ya cire hula ga tsare tsaren da aka yi bana, inda ya ba da shawarar a samar da wadatattun na’urar gwajin masu ciwon suga ga ma’aikatan jinya, a tsarin Hajjin badi, na gaba.

An kuma bayyana cewa, an kayyade nauyin kayan da alhazai za su dauka, wanda ya wuce haka kuma zai biya Riyal 15 a kowanne kilo ga alhazan Arewa, alhazan Kudu kuma za su ba da Riyal 16 a kowanne kilo.

Wakilin kamfanonin jiragen da za su yi jigilar alhazai kuma babban manajin darakta na kamfanin jiragen MedView Alhaji Mannir Bankole ya bayyana cewa jigilar komawa gida ta fi sauran ayyukan wahala, don haka ya shawarci shugabannin kula da harkokin alhazai su tabbatar da an shirya alhazan da za su tashi a waje daya awa 72 kafin lokacin tashi.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s