Ranar 6 Ga Watan Satumba Za’a Fara Jigilar Alhazan Najeriya Zuwa Gida

Shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa Abdullahi Mukhtar Muhammad ya bayyana ranar 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a fara jigilar dawo da alhazan Nijeriya gida bayan kammala aikin Hajjin bana. Muhammad ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kai wa alhazan Nijeriya a Mina, inda ya ce jirgi na farko zai baro Jidda ne da alhazan Jihar Gombe a ranar Alhamis mai zuwa.

Sannan shugaban ya kira da alhazan da su kasance cikin shiri su kuma taimaka wajen ba da hadin kai, domin ganin an kammala daukar alhazan lafiya.

A nasa jawabin wakilin alhazan Jihar Gombe ya ce za su ba hukumar alhazan Nijeriya NAHCON duk wani hadin kan da take bukata.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s