Alhazan Najeriya Biyar Sun Rasa Rayukansu A Kasar Saudiya

 

Alhazan Najeriya biyar da ke birnin Makka na kasar Saudia sun rasa rayukansu

Shugaban Hukumar Alhazai Ta Kasa NAHCON, Abdullahi Muktar Mallam ya sanar da  mutuwar mutanen hudu  a birnin na Makka.

Muhammad wanda yayi magana a wani taro da akayi kan shirye – shiryen ranar Arafat, amma kuma yaki yarda ya bayyana sunan mutanen da kuma abinda yayi sanadiyar mutuwarsu.

Yace za a iya fadin wannan bayani ne kawai bayan an sanar da iyalansu ta hanyar da ta dace.

Shugaban na NAHCON ya shawarci kafafen yada labarai kan kada su bayyana sunan mutanen inda yace hakan zai jefa iyalan mamatan cikin wani hali.

Mintoci kadan bayan ya gama jawabinsa sai Jagoran tawagar likitoci na NAHCON ya bayyana mutuwar maniyyaci daga jihar Kwara.

Alhazan Najeriya 81,200 ne suke gudanar aikin hajjin bana kuma dukkaninsu sun tattara a birnin Makka bayan da wasu suka kai ziyara Madina.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s