Kamfanonin Wayar Sadarwa Na Son A Kara Kudin Kiran Waya Da Na Intanet Da Kaso 100

Masu amfanin da wayar salula a kasarnan zasu biya kudi da yawa idan hukumar sadarwa ta kasa ta amince da bukatar kamfanonin wayar sadarwa na karin kudin kiran waya da kuma na amfani da Intanet da kaso 100.

Majiyoyi da yawa a hukumar sadarwa ta kasa NCC sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewa lallai kamfanonin wayar sadarwar  nayin sabon yinkuri na yin kira ga hukumar kan ta amince da karin kudin.

Wani ma’aikaci a hukumar ta NCC da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a bashi umarni yayi magana ba kan lamarin yace tun farkon wannan shekarar ne kamfanonin suke rokon hukumar da ta amince da karin  kudin da yan Najeriya suke biya a kowanne minti daya na kira da kuma kudin da ake siyan data ta shiga Intanet.

Yace kamfanonin suna korafin tsadar kayayyaki saboda haka baza su iya cigaba da karbar kudin da ake biya ba kan kiran waya da kuma datar shiga Intanet.

Sun kuma nuna yadda mutane suka rage yin kiran waya da kuma tura sako saboda yawan yin amfani dq  kafafen sadarwar zamani da suke bawa mutane damar kira, da tura sako kyauta ba tare da biyan kudi ba.

Masana sun ce saboda yadda kudin da kowanne mai amfani da waya ke kashewa a duk wata ke raguwa tun daga $ 14  a shekarar 2004 zuwa $4 kacal a wannan shekara saboda halin matsalar tattalin arziki, da kyar da gumin goshi kamfanonin suke iya samun riba.

Idan sabon karin ya tabbata kira tsakanin layukan wayar sadarwar kamfani daya zai koma N24 duk minti daya mai makon naira N12 da yake a yanzu yayin da kira tsakanin layukan kamfanoni zai koma N75.30k, kudin siyan  data 1GB da ake siya 1000 a yanzu zai koma 2000.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s