Abin Mamaki: Wasu Iyalai Sun Gano Yaronsu Bayan Shekara 25 Da Sace Shi a Sokoto

Wa su iyalai a Sokoto da ke zaune a Unguwar Kalfu da ke cikin garin Sokoto, sun bayyana jin dadin su da ganin dan uwan su bayan shekara 25 da sace shi. An gano shi a wani yanki da ake kira Zugu, Kpararate Gui dake Jamhuriyar Benin

Shi dai wannan bawan Allah mai suna biyu, inda a Sokoto ana kiran sa Ahmad Abbas, a can kuma ana kiran shi Aliyu Abbas, labarin shi nada ban al-ajabi.

Iyalan wannan Bawan Allah sun Kira ‘yan jarida kuma ya je ya ga wannan Bawan Allah, ya zanta da shi ta wani Bazabarme domin a yanzu ba ya jin Hausa sai Zabarmanci da Faransanci, kasancewar an sace shi tun yana dan shekara takwas a duniya.

A yayin da aka tambaye shi ko zai iya tuna wadanda suka sace shi, ya ce mutun biyu ne cikin mota, su na cikin tafiya da motar ta lalace sai dayan mutumin ya tare wata mota, suka shiga da sunan su je sayen abinci, sai mai motar Malam Aliyu Bunu, wanda shi direba ne da ke dauko kaya daga Sokoto zuwa Yamai ta Nijar, suna cikin tafiyar ya ga Yaron na kuka ya ce wa barawon wai wannan Yaron sa ne kuma yake ta kuka? Da suka isa gari na gaba da su, sai ya sawo abinci, sai ya sulale kasancewar ya ga asirin sa zai tonu.

Direban wanda yake dan asalin garin Zugu, Kparate Guit da ke cikin kasar Benin, ya tafi da yaron gidan maigari (Sufuyanu Bube) wanda yake shine Mai sarautar garin, a haka ya rike wannan yaron, har ya girma, yayi mai aure ya sanya shi Makaranta.

Da muka tambayi menene dalilin sanin wadannan ba su ne iyayen shi ba? Ya ce mutumin ne (Mai rikon shi) Allah ya yi masa rasuwa, sai aka ki raba gado da shi, a karshe matar marigayin ta sanar da shi cewa an sato shine, sai ya matsa ya na son sanin iyayen shi, a haka aka rubuta takarda zuwa ga kungiyar Zabarmawa mazauna Sokoto, su kuma suka sanya sanarwa a kafafen watsa labarai da ke cikin garin Sokoto, cewa idan da wanda ya san yaron shi ya bata shekara 25 da suka gabata, to ya zo ya yi bayani.

A haka daya daga cikin ‘yan uwan sa ya ji sanarwar suka zo suka gane shi ta wasu alamomi na jikinshi tun yana karami kana da alamar yayarshi da suke da kama.

Da muka tambayi batun iyali, sana’a da karatu.

Ya ce sun rabu da matar shi, Yaron da suka haifa ya koma, karatu kuwa, nan da ‘yan watanni zai kare kwaleji (SSCE), sana’a kuwa yana sayar atamfa da kayan sola.

Da aka neme jin wadanne kalubale ya fuskanta a lokacin yana can, yace surikar kirki ce bai samu ba.

Da muka nemi jin ra’ayin shi kan yadda yake ji tunda ya dawo gida, ya ce yana godiya ga Allah.

Shi dai wannan matashin zuwa yanzu Allah ya yi wa mahaifin shi rasuwa, amma za ku ga wasu hotunan da muka samo a lokacin yana karami tare da mahaifan shi. Zuwa yanzu kungiyar Zabarmawa mazauna Sokoto sun rubuta takarda wadda za a sanar da hukumomin kasar Bennin cewa wannan Bawan Allah, an gano dangin shi.

Da mukaji ta bakin yan uwan na shi kan yadda suka ji bayan dawowar dan uwan nasu, sun nuna jin dadin su sosai, kasancewar bayan bacewar shi sun yi ta nema ciki da wajen Sokoto.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s