Nmandi Kanu Yace Duk Wanda Yayi Kokarin Kama Shi To Ajalinsane Yazo 

Nmandi Kanu jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara yace kowane yayi niyar ka mashi to zai rasa ransa.

Ya bayyana haka ne a matsayin wani martani ga kiran da gwamnatin tarayya tayi na kotu ta soke belinsa da tabayar.

Bayan da ya shafe watanni 18 a gidan yari tun bayan da hukumar tsaro ta farin kaya DSS suka kama shi,  alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja mai shari’a Binta Nyako, ta bada belinsa a ranar  25 ga watan Afirilu.

Amma dan fafutukar ya saba dukkanin kaidojin belin da aka gindaya masa.

Da yake magana a makarantar fasaha ta maza dake garin Aba,na jihar Abia,Kanu yakai ziyara girmamawa ga mutanen da aka rawaito jami’an tsaro sun kashe a makarantar.

Kiran kafa kasar Biyafara abune da baza a iya dakatar dashi ba inda yakara da cewa kiran ” Wani sako ne daga Aljanna ”

Ya kuma dage kan cewar zasu kauracewa zaben gwamnan jihar Anambra har sai anyi zaben raba gardama da kungiyar take son ayi.

” Sun yi harbi sun kashe mu a wurare da dama dake cikin kasar Biyafara lokacin da mutane suke zanga-zangar neman a sakeni. Yayin da mutanenmu suke hutawa a kabarinsu bazan taba hutawa har sai an kafa kasar Biyafara ban damu da abinda suke fada a Abuja ba  da kuma wanda suke fada a Lagos.

” Ni dan Biyafara ne sai mun murkushe gidan ajiye namun daji (Najeriya). Wasu sakarkaru da basu da ilimi sun ce zasu kamani nace musu suzo ina kasar Biyafara idan daya daga cikinsu yabar kasar Biyafara da ransa to ya tabbatar wannan ba mu cika  kungiyar IPOB ba.A fada musu wannan ne abinda nace.

” A fadawa Buhari cewa ina Aba duk mutumin da yace zai kama Nmandi Kanu  a cikin kasar Biyafara zai mutu anan Ina kara tabbatar muku babu inda zanje gudun hijira,” Kanu yace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s