An Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Akan Lokaci

Hukumar Alhazan Naijeriya (NAHCON) ta kammala Jigilar maniyyatan kasar akan Lokaci, ba kamar yadda ake yada cewa an kara kwana daya domin a baiwa yan Najeriya damar kwasan Alhazan zuwa kasa mai tsarki ba.

Shugaban Hukumar ta kasa, Barista Abdullahi Mukhtar, yace tuni hukumar saudiyya ta rufe filin jirgin sama na Madina, amma Filin jirgin sama na jeddah ba’a rufe shi ba, har Jiragen Naijeriya suka sauka a wajen kafin wa’adin karkare jigilar Alhazan ya cika.

Mukhtar yace yana yabawa kamfanonin jirage musamman irin yadda sukayi kokari wajen cika alkawuran da suka dauka na kwasan Alhazan mu akan lokaci, ya kuma ce yadda akayi wannan jigila cikin sauri da kwanciyar hankali, haka za’a dawo da Alhazai gida Naijeriya insha Allah.

A karshe Mukhtar yayi kira ga Alhazan Naijeriya da suyi kokari wajen bin doka da oda, kuma su sanya kasar mu Naijeriya wajen addu’oin samun zaman lafiya, tare da sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin addu’oi na musamman, Allah ya bashi lafiya, ya kuma bashi ikon sauke nauyin dake bisa kansa na shugabanci

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s