Daga Zauren FIQHU: Fa’idar Fadin Kalmar “In Sha Allah”

Wani limamin masallacin juma’a na wani karamin gari a kasar Pakistan ya yi huduba kan fa’idar furta kalmar InshaAllahu duk lokacin da mutum ya kudiri yin wani aiki. 

Bayan kwanaki da yin hudubar, sai wani mutumin garin ya yi niyyar sayen saniya a kasuwar garin wanda yana kan hanya sai hadu da wani abokinsa  inda ya shaida masa niyyarsa amma kuma bai furta kalmar ‘ InshaAllahu ‘ ba, nan take abokin nasa ya ja hankalinsa game da muhimmancin furta kalmar amma sai mutumin ya nuna cewa ai babu bukatar ya furta kalmar saboda yana da kudin sayen saniyar.

A lokacin da ya isa kasuwar ya kuma dace da irin saniyar da yake bukata kuma ya yi ciniki aka sallama masa. Yana sa hannu cikin aljihunsa don ya ciro kudin, sai ya ji babu komi cikin aljihun, ashe lokacin da yake yawo cikin kasuwa yana duba irin saniyar da yake bukata, barawo ya lalube shi.

A lokacin da dillalin shanun ya tambaye shi a kan ko ya canja shawara ne kan sayen saniyar sai mutumin ya ce” InshaAllahu wani mako zan sayi saniyar”. Da ya koma gida, sai ya sanar da matarsa abin da ya faru kan yadda ya ki bin shawarar abokinsa na furta kalmar ” InshaAllahu”. Sai ya kara da cewa ” InshaAllahu ina son sayen saniya, InshaAllahu, barawo ya sace mani kudi kuma InshaAllahu wani mako zan yi sayi saniya”. Sai matarsa ta yi masa nuni da cewa ana furta kalmar ” InshaAllahu ne a kan aikin da za a yi, ba wanda ya rigaya ya auku ba.

DARASI: Duk abin da mutum zai aikata, ya kudura a ransa da cewa sai da ikon Ubangiji ne abin nan zai iya yiwuwa, amma ba da kafinsa ko dabararsa ba.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s