BERAYE SUN MAMAYE OFFISHIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI

 

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RAHOTANNI daga fadar shugaban kasar Nijeriya na bayanin cewa Beraye sun yi mummunar barna a ofishin shugaba Muhammadu Buhari a tsawon watanni uku da ya yi baya amfani da ofishin.

Mai yi wa shugaban kasa hidima a game da harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana wa manema labarai hakan inda ya ce sakamakon barnar da kwari da beraye suka yi ya haifar da wannan matsalar ta lalacewar wayoyi da na’urori da wasu kayayyaki.
“A yanzu haka an ba kamfanin Julius Barger kwangilar aiwatar da gyara kuma shugaban zai rika yin aiki daga wani ofishin da ke gidansa, har zuwa lokacin da za a kammala aikin”.
Shugaba Buhari dai an bayyana cewa zai rika yin aiki daga gida akalla na tsawon watanni uku har zuwa lokacin da za a kammala aikin.
Da manema labarai na yi wa Malam Garba Shehu tambayar shin ta yaya tun dadewa ba a bude ofishin ba? Sai ya amsa da cewa ta yaya wani mutum zai zo ya ce a bude masa ofishin shugaban kasa?
Kuma ya kara da gayawa manema labaran cewa ko a lokacin da yake magana da su shugaba Buhari na can yana ganawa da dukkan shugabannin tsaron kasar baki daya a ofishin da yake aiki a halin yanzu.
Shehu ya ce akwai lokacin da Abacha ya rika yin aiki daga gida har shekara daya don haka za a iya yin aiki daga gida ba sabon abu ba ne.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s