DAN MAJALISA YA TONA ASIRIN GWAMNATIN SOKOTO

 

Dan Majalisar mai wakiltar karamar hukumar mulkin Gudu a Majalisar Dokoki ta jihar Sokoto, Hon. Sani Yakubu ya bayyana wasu asirran gwamnatin jihar Sokoto. Dan Majalisar ya fadi hakan a wata hira da aka yi dashi a cikin shirin Sakkwatawa Kwallahiya na gidan rediyon Vision FM dake Sokoto.

Kadan daga cikin abinda Hon. Sani yace “Bashin Biliyan 120 aka ciwoma Sakkwatawa tare da hadin kan Shugaban Majalisa Hon. Mai Daji wanda mu ba mu san yaushe za’akai ana biya wannan bashi ba, kuma ta yaya ma zamu biya wannan bashi? Yaushe? Shekara nawa? Dami Sakkwatawa zamu biya wannan bashin? Haba!”

“Anci bashin Biliyan 120 ba’a gayamana inda aka je dasu ba, kuma an bada kudin Paris Club sunki fadin inda aka je dasu. Sannan kuma gaba daya basu ma yin maganar kudin Bail Out din Sakkwatawa”

“Duk bashin da aka ciwo a Jahar Sokoto da Shugaban Majalisar Hon. Mai Daji ake rabawa,  shi yasa kullum yake hana binciken da ake son yi wanda Hon. Malami Bajare ma da yake Shugaban bicikar kudin gwamnati, da yace zaiyi bincike sai suka shiryamasa makirci suka dauke shi daga wurin suka maidashi wani wuri sannan suka sanya wanda bai iya binciken komai”

“Wallahi Tallahi sai da muka zauna da Speaker Mai Daji kamin mu bashi Speaker cewa ba zai zama Dan-kwangilar kowa ba kuma ya yi rantsuwa da Allah cewa bazai zama ba, amma ga abinda yake yi yanzu”

“Ina gayawa Sakkwatawa cewa suyi alkalanci da kansu kuma duk mai nema na don samun hujjojin abinda nake fada، yazo ina zama office dina har karfe 5pm na yamma kuma lambobin wayana suna cikin garin Sokoto ga mutane daban daban”

MADOGARA: Hon. Naseer Bazza

 

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s