Shekau Ya Gargadi Mazauna Birnin Maiduguri A Wani Sabon Fefan Bidiyo 

Abubakar Shekau,Jagoran kungiyar Boko Haram, yayi barazanar kai sababbin hare-hare  akan birnin Maiduguri.

Birnin na Maiduguri mai dogon tarihi ya fuskanci hare-hare da dama daga kungiyar Boko Haram cikin wata dayan da ya gabata.

A wani sabon bidiyo da kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta samu Shekau yayi barazanar sa kafar wando daya da mutanen dake zaune a birnin Maiduguri  ” Saboda yadda suke cudanya da kafirai. ”

” Kun gama ku mutanen Maiduguri, sai mun gama daku saboda yadda kuka zabi bin kafirai da kuma rungumar dimokwaradiya,” a cewar shugaban kungiyar wanda yayi magana da harshen larabci.

Shekau ya kuma karyata ikirarin da sojoji su kayi cewa ya samu rauni a wani hari da aka kai masa ta sama .

Yakara da cewa idan da sojoji sunyi nasarar kamashi, akidarsa zata cigaba da wanzuwa ko bayan mutuwarsa.

” Lafiya kalau nake, babu wani abu da ya same ni kai yanzu ma nafi jin kwarin jiki fiye da yadda nake a baya,” yace.

“Ni ba komai bane, ko da kun kama ni baza ku iya kama addinin Allah ba. Zaku iya kamani a yau saboda ni ba komai bane. amma kuma hakan bazai dakatar da addinin Allah ba wanda muka ba muhimmanci.Wannan bindigar da nake rike da ita ba komai bace  mun dogara ne da karfin Allah.”

A ranar 22 ga watan Yuli ne babban hafsan sojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai,ya bawa sojoji wa’adin kwana 40 kan su kamo shekau a raye ko kuma a mace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s