Har Yanzu Gwamnatin APC Bata Tsinana Komai Ba – Johnathan 

Tsohon Shugaban Nijeriya Dr Goodluck Ebele Jonathan a yayin gabatar da nasa jawabin a wajen babban taron PDP na kasa a garin Abuja, ya bayyana cewa gwamnatin APC ba ta tsinanawa talakawa komai.

Ga wasu daga cikin kalaman Jonathan a yayin taron;
*️ Good Ebele Jonathan a cikin jawabinsa ya ce shi bai ga abunda jam’iyyar APC ta sakawa talakawan Nigeriya da shi ba sai wahala duk da ikirarin da take yi cewa gwamnatinta ta talakawa ce, haka kuma ya kara da cewa jam’iyyar APC ta kassara Nijeriya har ta rasa inda za ta kama balle ta fito da hanyar sakawa talakawanta,

* Don haka ya zama wajibi ga yan’ Nijeriya da su yi wa kansu mafita su fita batun APC su kama PDP 2019 saboda yanzu kowa ya ga kamun ludayinta babu abunda ta’iya sai Wasa da hankalin mutanen Nijeriya, koda yaushe sai yada farfaganda yake yi cewa ta yi abun kirki amma ba’a ganin komai akasa.

*Jonathan ya kara da cewa ita jam’iyyar APC ta kasa cika alkawarinta, don haka ba wani dalilin da zai sa a cigaba da bibiyarta don ba ta sakawa talakawanta ba, balle ta kawowa kasarta cigaba. Kullum sai maganar Noma suke yi amma sun kasa fitowa da hanyar taimakon manoma na asali.

*Talakawa sun zabi jam’iyyar APC da tunanin za ta warware wasu matsaloli nata amma har yanzu ba wani abu da talakawa suka morewa dashi acikin APC sai Tsadat rayuwa, da yunwa, da fatara, kowa sai kuka yake yi kuma har yanzu bawani bayani akasa dun haka bai kamanta APC ta cigaba da wahalar da ‘yan kasa ba.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s