” CIKA AIKI NA WAKILI” Inji Mutanen Karamar Hukumar Mulkin Illela.

Kwamitin karba da tattara kudaden shige da fice (Revenue Committee) na karamar hukumar mulkin Illela , ya fara gudanarda a yukkan shinfida tituna da cike makwantun ruwa a cikin kasuwar Illela.

Wannan muhimmin aiki da Jama’a musamman Yan Kasuwa suka jima suna jiran faruwa sa, ya samu gudanarwa ne da kudaden da ake karba daga wajen jama’a Yan Kasuwa.

Aikin wanda aka soma Ranar assabar 12/8/2017 an fara shine a Kabale Market wato ma’ana kasuwar ‘Yan Dankali da ‘Yan Rake da Tanka, bayan an Kammala aikin wadannan wuraren, za’ a ci gaba da aikin zuwa kasuwar ‘Yan Hatsi da Karar Bisashe da wajen ‘Yan kayan Ruwa.

Kamar yadda Sakataren wannan Kwamiti Alh.  NASIRU SHEHU (OSAMA) ya shaidama Jami’inmu, dazarar an samu Kammala wannan muhimmin aiki, za’a ci gaba da gyaran magudanun Ruwa da Hanyoyi na cikin Garin Illela da Kewaye.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s