Ko Buhari Ya Dawo Ko Kuma Yayi Murabus – Charley Boy 

 

Mawakin nan Charley Boy a ranar Litinin zai jagoranci zanga-zanga inda za su bukaci Buhari ya dawo gida ko kuma yayi murabus. 

A wata sanarwa da wasu hadakar kungiyoyin fararen hula suka fitar ,tace zanga-zangar za  a gudanar da ita ne a Abuja.

Kungiyoyin sun ce za su cigaba da gudanar da zanga-zangar tare da zaman dirshan a dandalin da ake kira Unity Fountain dake Abuja, har sai shugaban kasar ya dawo ko kuma yayi murabus.

” Yau kwanaki 90 tun bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya bar kasarnan zuwa London domin jinya, ” sanarwar tace.

” Muna wannan rubutu ne domin sanar da dukkanin mutane, kafafen yada labarai na gida da kuma kasashen waje cewa Charles Oputa da akafi sani da Charley Boy, da kuma wasu fitattun yan Najeriya za su jagoranci zaman dirshan din da za a fara daga ranar Litinin da karfe goma na safe a dandalin Unity Fountain.

“Za a fara kaddamar da zaman da wani jerin gwano daga dandalin zuwa fadar Aso Rock da misalin karfe 9.” sanarwar tace.

Haka kuma za a gudanar da makamancin irin wannan zama a gaban gidan da Buhari yake zaune a birnin London.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s