Buhari ne ya kirkira matsalolin ‘yansandan kasar nan – Sarkin jihar Legas

Sarkin Legas Oba Rilwan Akiolu yace shugaba Buhari ne yayi sanidiyar tabarbarewar ayyukan rundunar yan sandan Najeriya. A cewar sa gwamnatin tarayya a karkashin mulkin shugaba Buhari a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985 ta dena baiwa rundunar kulawa da kudin gudanarwa domin tana zargin rundunar tana yi mata zagon kasa, wannan ne yayi sanadiyar tabarbarewan rundunar.

Sarkin amma yayi kira ga shugaba Buhari da ya maida hankali wajen farfado ya martabar rundunar yan sandan tunda yanzu ya dawo a matsayin shugaba na mulkin dimokuradiyya. Akiolu, wanda tsohon sifeta janar ne na rundunar ‘yan sandan ya fadi wannan maganganun ne a wani taro da akayi a ranar juma’a mai taken “Nemo hanyoyin da za’a magence matsalolin tsaro da ke tasowa”. Sifetan rundunar yan sanda Ibrahim Idris ne ya shirya taron.

Yace: “Soji ne sukayi sanadiyan tabarbarewar rundunar yan sanda, matsalan ya samo a asalin ne a shekarar 1984 a lokacin shugaba Buhari ke mulki. A lokacin sunce Sunday Adewuyi yana son ya karbe mulki, nayi musu bayanin hakan bazai yiwu ba amma ba su saurare ni ba. “Anyi wani taro a Abuja inda shugaba Buhari yace mana gwamnati zata horar da sababin yan sanda guda 10,000. Abin ya faranta min rai sosai.”

Akiola ya cigaba da cewa ya shawarci tsohon Shugaba Abdulsalami Abubakar a shekarar 1998 da ya kara yawan jami’an rundunar a manyan titunan kasar nan domin yaki da fashi da makami. Amma amsar da ya bani shine, “Kana son ne in karkatar da dukkan dukiyar kasar zuwa rundunar yan sanda?”

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s