Archbishop na Canterbury,Justin Welby ya ziyarci shugaban kasa Muhammad Buhari, A birnin London. Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da yafitar jiya.
Adesina yace Buhari da Welby abokaine wadanda suke matukar girmama juna, ya rawaito Archbishop Welby na cewa yaji dadi yadda yaga shugaba Buhari yana murmurewa cikin sauri daga rashin lafiyar da yake fama da ita, wannan yana nuna karfin da Allah yake da shi na warkar da mutum daga cuta da kuma ansa addu’ar miliyoyin mutane a duniya dake yin addu’ar fatan warkewar shugaban.
Mai magana da yawun shugaban kasar yace Archbishop Welby,yayi alkawarin cigaba da yiwa Buhari da Najeriya addu’a .Adesina ya kuma rawaito Buhari yana godewa Archbishop Welby wanda ya lura da cewa ako da yaushe yana tare dashi musamman a irin wannan lokaci da yake cikin wani hali