Musulma Ta Tsaya Takarar Neman Kejarar Majalisar Dattijan Amurka

A karon farko wata musulma ta tsaya takarar neman kujerar asanata a kasar Amurka daga jahar Arizona.

Shafin sadarwa usnews ya bayar da rahoton cewa, Didar Abbud musulma ‘yar takarar neman kujera a majalisar dattijan Amurka daga jahar Arizona karkashin inuwar jam’iyyar Democrat, ta mayar da martini dangane da sukar ta da wasu ke a shafukan yanar gizo.

Didar ta bayyana cewa a matsayin na ‘yar kasar Amurka mai cikakken ‘yanci tana da hakkin tsayawa takara, wannan kuma shi ne ‘yanci na demokradiyya, saboda haka babu abin da za ta boye dangane da addinta ko akidarta.

Ta ci gaba da cewa abin da ke da muhimamnci shi ne yin aiki bisa abin da dimukradiyya ta ginu a kansa, tare da yin adalcia tsakanin ‘yan kasa da yi musu bisa da kuma cika musu alkawali, amma addini ko akida kowa yana da nasa addini ko akida da ya yi imani da ita.

Kotun jahar Arizona ta yi jinjinawa wannan ‘yar takara musulma, tare da bayyana kalamanta da cwa suna kan hanya, kuma hakan abin koyi ne ga duk dan kasa na gari.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s