Karuwai Sun Bukaci Gwamnatin Najeriya Data Halasta Sana’arsu Ta Karuwanci

Masu sana’ar karuwanci a Nigeria sun nemi Gwamnati ta halasta sana’ar bin karuwanci a kasar, sannan a daina nuna tsangwama ga masu yin sana’ar. 

Kiran hakan ya fito ne daga shugabar kungiyar mata karuwai ta Nigeria, Amaka Anemo, Amaka tace halasta bin maza a matsayi sana’a zai rage yaduwar cutar sida sannan zai bayar da kariya ga masu yin sana’ar.

Shugabar matar tace sau tari jami’an doka idan suka kama su suna karbar kudade ne hannunsu a yayinda lokuta da dama kuma suke kwana dasu a matsayin fansa. Tace galibi kuma jami’an dokar basa amfani da kariya wanda hakan ka’iya zama hadari

Hausa times ta ruwaito Amaka na fadin, akwai fitattun mutane masu nuna kyamar sana’ar a bayyane amma kuma suna so a boye, kuma mafi yawa sune manyan kwastomomi.

Tace a irin haka sai miji ya lallaba ya je ya kwaso cuta yaje ya shafawa iyalinsa ko budurwarsa wacce itama zaka samu tana da nata saurayin a boye itama ta goga masa. Tace amma idan aka halasta sana’ar karuwan zasu fi jin dadi wajen tsaftace sana’ar tasu da inganta ta kuma zasu fi samu a kula da kiwon lafiyarsu
Shin kun goyi baya a halasta sana’ar karuwanci a Nigeria?

1 thought on “Karuwai Sun Bukaci Gwamnatin Najeriya Data Halasta Sana’arsu Ta Karuwanci

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s