PDP Zata Kulla Kawance Da Jam’iyu   16 Kafin Zaben 2019 – Makarfi

Shugaban rikon jam’iyar PDP na kasa, Ahmad Makarfi yace jam’iyar na tattaunawa da wasu jam’iyu 16 a kokarin da jam’iyar take na karbar mulki daga hannun APC a zaben 2019.

Makarfi ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da yan jaridu a Abuja, makasudin tattaunawar shine na yadda za a  samar da hadakar jam’iyu daza su kawar da jam’iyar APC  a zaben 2019.

” Muna magana da jami’yu sama da 16 domin muga yadda zamu hada kai muyi aiki tare.

“Da zarar mun hada kai,to zamu iya karbar gwamnati,” tsohon gwamnan kadunan yace.

Da aka tambayeshi kan rashin lafiyar shugaban kasa,Makarfi yace maganar ta kawo rashin tabbas  a gwamnati.

Yace”kada mu maida rashin lafiyar shugaban kasa ta zama siyasa, amma kuma baza mu gujewa gaskiyar cewa rashin lafiyar tasa yakawo nakasu a harkar gwamnati.

“Muna da mukaddashin shugaban kasa  da tsarin mulki ya bawa cikakken ikon gudanar da mulki,amma kullum uzuri suke bayarwa.

“Babu ta yadda zasu samar da hadin kai ta haka, har takai da shugabanci na gari. “

1 thought on “PDP Zata Kulla Kawance Da Jam’iyu   16 Kafin Zaben 2019 – Makarfi

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s