Lauya Ya Shigar Da Kara Kotu Kan Rashin Lafiyar Buhari 

Wannnan ce kara ta biyu da aka shigar gaban kotu dake bukatar  kotu ta umarci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan ya kafa kwamiti da zaiyi bincike kan rashin lafiyar Shugaban kasa Buhari,bayan karar da wani Lauya dan Najeriya mazaunin kasar Amurika,Toyin Dawodu ya shigar.

Badai asa ranar sauraron karar ba.

Wani Lauya mazaunin Abuja ya shigar da kara gaban babbar  kotun tarayya dake Abuja, yana neman kotun ta bayyana Buhari a matsayin wanda bazai iya cigaba da gudanar da mulki ba.

Kingdom Okere ya shigar da kara gaban kotun inda ya nemi ta umarci majalisar zartarwa ta kasa da ta zartar da kudirin cewa Buhari ya gaza bazai iya cigaba da gudanar da harkokin mulki ba.

Okere wanda Darakta ne na gidauniyar kare hakkin biladama ta Kindom,  ya hada da mukaddashin Shugaban kasa, Ministan Shari’a da kuma majalisar kasa a cikin wadanda yake kara.

Yayi ikirarin cewa shugaban kasa ya shafe sama da kwanaki 60 yana jinya.

Wannnan ce kara ta biyu da aka shigar gaban kotu dake bukatar  kotu ta umarci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan ya kafa kwamiti da zaiyi bincike kan rashin lafiyar Shugaban kasa Buhari,bayan karar da wani Lauya dan Najeriya mazaunin kasar Amurika,Toyin Dawodu ya shigar.

Badai asa ranar sauraron karar ba.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s