DA DUMI-DUMI: An kara wa sojoji 6000 masu yaki da Boko Haram mukamai

Wani jawabi da kakakin rundunar sojojin kasar nan, Sani Usman ya fitar, ya ce a yau ne Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai ya amince da karin girman.

“Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Y. Buratai, ya amince da Karin girma ga sojoji 6,199 wadanda ke aiki karkashin Operation Lafiya dole, masu yaki da Boko Haram.

“An yi wannan karin ne ga duk kowane mukami jami’an su ke, daga Lanse Kofur zuwa Waran Ofisa na sojojin Najeriya.” Inji Usman, mai mukamin Burgediya Janar.

Usman ya bayar da jadawalin yawan wadanda aka yi wa karin girman kamar haka:

1. Babban Saje zuwa Waran Ofisa –329.

2. Saje zuwa Babban Saje –371.

3. Kofur zuwa Saje –707.

4. Lanse Kofur zuwa Kofur –1,290.

5. Karabiti zuwa Lanse Kofur –3,502.

“Babban Hafsan Hafsoshi ya na kara taya ku murna, tare da jan hankalin ku wajen kara himma dominn a kakkabe Boko Haram a Arewa maso Gabas.” Cewar kakakin askarawan.

Tun cikin 2009 ne sojoji ke faman yaki da Boko Haram, a lokacin da ‘yan kungiyar su ka fara sunkuru.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s