Ana Cigaba da Samun Yayan  Kungiyar Boko Haram Dake Mika Wuya Ga Sojoji 

Rundunar sojin Najeriya a ranar Asabar tace mutane uku yan kungiyar Boko Haram suka mika wuya ga rundunar rundunar dake aiki karkashin aikin samar da tsaro na Operation Lafiya Dole a Buni Yari dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe. 

A wata sanarwa mai magana da yawun rundunar,Sani Usman yace yan ta’addar da suka tuba sun fito ne daga kungiyar Boko Haram dake karkashin jagorancin Mamman Nur,Sun ajiye aiyukan ta’addanci bayan da suka gane shirme da kuskuren da suke tafkawa basa kuma so su cigaba da aikata haka.

” Da safiyar yau, Asabar 22 ga watan Yulin 2017 , mutane uku da suka bayyana kansu a matsayin yan  kungiyar ta’addanci ta Boko Haram,Usman Ali mai shekaru 23, Ibrahim Matukur mai shekaru 13 da kuma Usman Hussaini mai shekaru 25 sun mika kansu ga Birged ta 27 dake aiki karkashin aikin samar da tsaro na Operation Lafiya dole a garin Buni Yari dake  karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

” Sauran sune Ali Baba dan shekara 25,Modu Wakil dan shekara 15,Usman Muhammad dan shekara 47, Modu Konto dan shekara 20  da kuma Isa Ali dan shekara 25.

“Bayan binciken farko da akayi musu yan ta’addar da suka mika wuya sun ce sunfito ne daga kungiyar Boko Haram bangaren shugabanncin Mamman Nur.Kuma sun mika wuya ne bayan da suka gane shirmen da sukayi a baya ba kuma sa bukatar sake kuskure irin haka anan gaba.

” Sun kuma kara da cewa sun tsere ne daga maboyar kungiyar dake kauyen Buk a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno, inda suka ce akwai yan kungiyar da dama da suke son mika wuya saboda irin wahalar da suke fuskanta.

“Sun roki afuwa da kuma yafiya daga jama’a inda suka ce an batar musu da tunani kan cewar abin da suke fada akai gaskiya ne.

” Sun shawarci rundunar soji kan tayi kokarin  isa gun yan ta’addar dake cikin daji tun da suna so  su mika wuya.” Usman yace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s