SENATOR GOBIR: TALLAFI ZUWA GA AL’UMMAR DA SUKA SAMU IFTILA’I A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

SENATOR GOBIR: TALLAFI ZUWA GA AL’UMMAR DA SUKA SAMU IFTILA’I A KARAMAR HUKUMAR MULKIN ILLELA.

Senator Gobir ya bayarda tallafin buhuhuwan Siminti, Tirela biyu (Tone Sittin – 60 / 1200) da Naira Miliyan Daya don rabawa ga ilahirin Mutanen da Allah ya kawo ma Iftila’in hasarar Rayukkansu, Gidajensu da Dukiyoyinsu a sanadiyar Ruwan sama da Iska da akayi a kwanan baya.

A sa’ilin da yake jawabi akan kwamitotan damn aka kafa don gudanar da rabe raben kayan na tallafi, Shugaban karamar hukumar mulkin Illela ya kara jajanta ma al’ummar da abin ya shafa tare da Jan hankalin dukkan Kwamitochi akan jajircewarsu tare da jin tsoron Allah a lokacin da suke kokarin gabatar da shi wannan muhimmin aiki.

Maigirma Wakilin Sarkin Rafin Illela ya jinjinawa Maigirma Senator Gobir akan namijin kokarin da ya nuna na tausayawa ga wadannan bayin Allah.

Ya kuma ja hankalin ‘Yan kwamiti akan jin tsoron Allah a sa’ilin da suke gudanar da nasu aiki.

Dukkan wakilai daga gundumomi ukku da abin ya shafa sun samu wakilci a cikin taron. Gundumomin kuwa sune, Mazabar Illela, Mazabar Araba da Mazabar Rungumawar Gatti.

Wannan taron kamar yadda za’a gani a cikin Hotuna, ya samu halartar : Hon. Abdullahi Haruna Illela – Chairman Illela LG, dukkan Kansiloli goma sha daya, Sakataren Karamar hukumar mulkin Illela, Shugaban Sashen Mulki (DPM) Illela LG, Shugaban Sashen Ayukka (Director Works) Illela LG, Shugaban sashen jin dadin Jama’a (Director Social), Maigirma Wakilin Sarkin Rafin Illela, Maigirma Wakilin Sarkin Arewan Araba, Alh. Abubakar Abdullahi (Ubandawakin Illela), Aminu A. Musa (Galadiman Illela), dukkan Jami’an tsaro, Yan Siyasa da Yan Kasuwa.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s