Buhari Zai Dawo Gida Najeriya Ranar 27 Ga Watan Yuli – Sahara Reporters 

Sahara Reporters ta bayyana cewa na kewaye da fadar shugaban kasa zasu dawo da shugaba Buhari kasar a watan Yuli.

Shahararriyar jaridar nan ta wato Sahara Reporters ta fitar da wani sabon rahoto kan yadda na kewaye da fadar shugaban kasa ke kokarin dawo da shugaba Muhammadu Buhari gida Najeriya daga London inda ya ke jinya.

Sahara Reporters ta rawaito cewa, makusanta shugaba Buhari sun bai wa uwargidar shugaban kasar cikakkiyar damar ganin mijin nata a yanzu sannan kuma sun saka ranar da shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a matsayin ranar 27 ga watan Yuli, 2017.

Zuwa yanzu dai Shugaba Buhari ya kwashe tsawon kwanaki 73 a birnin Landan, inda ya ke jinyar wata lalura da ba a bayyanawa jama’a cikakken bayani a kan ta ba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar gida Najeriya zuwa birnin London a ranar 7 ga watan Mayu, 2017

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s