An Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ta Saki Sambo Dasuki 

An shawarci gwamnatin tarayya da ta saki tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Sambo Dasuki kana ta saka ido akansa idan ana tunanin zai zama barazana. 

A wata sanarwa da aka fitar a Abuja, wani masani kan harkar tsaro kuma jigo a jam’iyar APC, Cif Jackson Lekan Ojo,yace cigaba da tsare Dasuki ya saba ka’ida, ana kuma ganin haka a matsayin wata bita da kullin siyasa.

Cif Ojo,  wanda shine jami’in tsare-tsare na kasa a kungiyar Yoruba Youth Alliance yace dole ne kowa ya goyi bayan yaki da cin hanci amma ya shawarci gwamnatin tarayya kada ta maida kanta abar dariya.

“Wannan Yariman dan gidan sarautar daular Sokoto, babu wata Kotu da ta aiyana shi da laifin cin amanar kasa, da har zai sa a tsare shi  lokaci  mai tsawo.Yakamata a bada belinsa koda da wasu ka’idoji ne. Har yanzu babu wata kotu da ta same shi da laifi.

” Ina kuma so na bada shawarar cewa a sake shi,  sannan a saka masa matakan tsaro   idan ana ganin zai iya zama barazana ga harkar tsaron kasa, ” yace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s