WANNAN LABARIN YA GIRGIZA NI MATUQA

WANNAN LABARIN YA GIRGIZA NI MATUQA

Wani Bawan ALLAH Da Yake Kan Gargarar MUTUWA, Sai Dangi Suka Kewaye Shi Suna
Ta Kuka.
.Sai Ya Ce:”Ku Tashe Ni Zaune”
.
Sai Suka Zaunar Da Shi Sai Ya Fuskance Su
Ya Dubi Mahaifinsa Ya Ce:”Baba! Me Yasa
Kake Kukan Rabuwa Da Ni???”
.
Ya Ce:”Ina Jimamin Rashinka Da Yadda Zanyi
Da Kewarka Bayan Ka Rasu!”
.
Sai Ya Juya Ga Mahaifiyarsa Ya Ce:”Umma!
Me Yasa Kike Kukan Rasa Ni???”
Ta Ce:”Saboda Zan Shiga Quncin Rayuwar
Rasaka!”
.
Sai Ya Juya Ga Matarsa Kefa Me Yasa Ki
Kuka???
.
Sai Ta Ce:”Zan Rasa Dadin Zaman Da Muka Yi
Gashi Kuma Ban San Hannun Wanda Zan
Fada Ba”.
.
Sai Ya Juya Ga ‘Yayansa Kufa Me Yasa Ku
Kuka???
.
Suka Ce:”Saboda Zamu Zama Marayu Bamu
San Irin Wahalar Da Zamu Shigaba Bayan
Baka Nan”
.
Don Allah Idan ku Karanta ku dinga yin Like & Comment ko kuma kuyi Share domin ‘yan uwan Mu su Amfana.
.
Daga Nan Sai Ya Dube Su Ya Fashe Da
Matsanancin Kuka Gaba Daya Suka Dube Shi
Kai Kuma Me Yasa Ka Kuka???
.
Ya Ce:”Naga Kowa Yana Kukan Rasa Ni Ne
Saboda Bukatar Qashin Kansa.
.
Shin a Cikinku Akwai Wanda Yake Kuka
Saboda Doguwar Tafiyar Dake Gabana???
.
Koko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda
Rashin
Isashshen Guzuri Na???
.
Ko Akwai Wanda Yayi Kuka Don Za’a
Turbudani a Turbaya???
.
Ko Abin Da Zan Tarar Na Mummunan
Hisabi???
.
Ko Ko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda
Tsayuwata a Gaban Rabbil Izzati Bansan Me
Zan Tarar Ba???
.
Daga Nan Sai Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Sai
Sukai Kansa Suka Juya Shi Sai Sukaga Ashe
Har Rai Yayi Halinsa Ya Rasu!.
.
HAQIQA DUNIYA BATA DA TABBAS!

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s